Nehemiah 13:22 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai na umarci Lawiyawa su tsarkake kansu su kuma tafi su yi tsaron ƙofofi don a kiyaye ranar Asabbaci da tsarki. Ka tuna da ni saboda wannan shi ma, ya Allahna, ka nuna mini jinƙai bisa ga madawwamiyar ƙaunarka.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ نَعُمَرْثِ لَوِيَاوَا سُڟَبْتَثٜىٰ كَنْسُ بِسَغَ دُواْكَا، سُتَڢِے سُيِ غَادِنْ ڧُواْڢُواْڢِنْ دُواْمِنْ سُتَبَّتَرْ أَنْكِيَايٜىٰ رَانَرْ هُوتُ تَمَكُواْ دَ ڟَرْكِے؞ «يَا اللَّهْ نَا، تُنَ دَنِے سَبُواْدَ وَنَّنْ؞ بَرِ كَيِمِنِ جِنْڧَيْ بِسَغَ يَوَنْ ڧَوْنَرْكَ مَرَرْ ثَنْجَاوَا؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai kuma na umarci Lawiyawa su tsarkake kansu, su yi tsaron ƙofofin don a kiyaye ranar Asabar da tsarki. “Ya Allahna, ka tuna da wannan aiki nawa, ka rayar da ni saboda girman madawwamiyar ƙaunarka.”