Nehemiah 13:5 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
ya kuma tanada masa babban ɗakin da dā ake ajiyar hadayun hatsi da turare da kayayyaki haikali, da kuma zakan hatsi, sabon ruwan inabi da kuma mai da aka umarta don Lawiyawa, mawaƙa da kuma matsaran ƙofofi, da kuma sadakoki domin firistoci.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ يَبَا تُواْبِيَ بَبَّنْ طَاكِنْ دَ دَا عَكَنْ أَجِيٜىٰ بَايَرْوَ تَهَڟِ دَ تَتُرَارٜىٰ دَ تَكَايَنْ دَ عَكَيِ أَمْڢَانِ دَسُو أَ هَيْكَلِ دَ كُمَ زَكَّ تَهَڟِ دَ تَسَابُوانْ ضُوً إِنَبِے دَ تَمَنْ ظَيْتُنْ دَ عَكَ عُمَرْتَ دُواْمِنْ لَوِيَاوَا دَ مَوَاڧَ دَ مَاسُ غَادِنْ ڧُواْڢُواْڢِنْ هَيْكَلِ دَ كُمَ بَايَرْوَ دُواْمِنْ ڢِرِسْتُواْثِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
ya shirya wa Tobiya babban ɗaki inda dā aka ajiye hadaya ta gari, da turare, da tasoshi, da zakar hatsi, da ruwan inabi, da mai, waɗanda aka umarta a ba Lawiyawa, da mawaƙa, da masu tsaron ƙofofi, da inda aka ajiye sadakokin da ake ba firistoci.