Nehemiah 2:1 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A watan Nisan a shekara ta ashirin ta mulkin Sarki Artazerzes, sa’ad aka kawo masa ruwan inabi, sai na karɓa na ba shi. Ban taɓa ɓata fuskata a gabansa ba, sai wannan karo.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَايَنْ وَتَا حُطُ، وَتُواْ أَوَتَنْ نِسَنْ، أَ شٜىٰكَرَا تَعَشِرِنْ تَمُلْكٍ سَرْكِے أَرْتَظٜىٰكْظٜىٰسْ، سَعَدَّ عَكَ شِرْيَ ضُوً إِنَبِنْسَ، سَيْ نَكَيْ نَمِيڧَوَ سَرْكِے؞ سَرْكِے كُوَ بَيْتَٻَ غَنِينَ دَ ٻَاتَنْ ڢُسْكَ أَغَبَنْسَبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ni kuwa ina riƙe da finjalin sarki. Wata rana a watan Nisan, a shekara ta ashirin ta sarautar sarki Artashate, sa'ad da na kai masa ruwan inabi, sai na ɗauki ruwan inabin, na ba shi. Ni ban taɓa ɓata fuskata a gabansa a dā ba, sai wannan karo.