Nehemiah 2:5 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
na kuwa ba wa sarki amsa, na ce, “In ya gamshi sarki, in kuma bawanka ya sami tagomashi a idonka, bari ka aike ni in tafi ƙasar Yahuda, birnin da aka binne kakannina, domin in sāke gina shi.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً نَڢَطَا وَسَرْكِے نَثٜىٰ «عِدَنْ يَا غَمْشٜىٰكَ، يَا سَرْكِے، عِدَنْ كُمَ نِے بَاوَنْكَ نَا سَامِ أَلْحٜىٰرِ دَغَ غَرٜىٰكَ، بَرِ كَعَيْكٜىٰنِ إِنْ تَڢِے ڧَسَرْ يَهُودَ، بِرْنِنْ دَ عَكَ بِنّٜىٰ كَاكَنِّنَ، دُواْمِنْ إِنْ سَاكٜىٰ غِنَا بِرْنِنْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
sa'an nan na ce wa sarki, “Idan ka yarda, idan kuma na sami tagomashi a wurinka, ya sarki, ka yardar mini in tafi Yahuza, birnin kakannina, inda makabartarsu take domin in sāke gina shi.”