Nehemiah 2:7 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Na kuma ce masa, “In ya gamshi sarki, zai yi kyau in sami wasiƙu zuwa ga gwamnonin Kewayen Kogin Yuferites, domin su tanada kāriya har sai na isa Yahuda?
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ نَڢَطَا وَسَرْكِے نَثٜىٰ «عِدَنْ يَاغَمْشٜىٰكَ، يَا سَرْكِے، سَيْ كَبَانِ وَسِيڧُ ذُوَاغَ ڠُومْنُواْنِنْ يَنْكِنْ ڧٜىٰتَرٜىٰنْ كُواْغِنْ يُڢِرٜىٰتِسْ دُواْمِنْ سُسَا إِنْوُثٜىٰ لَاڢِيَ حَرْ ذُوَا يَهُودَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan na ce wa sarki, “Idan sarki ya yarda, sai a ba ni takarda zuwa ga masu mulki da suke a lardin Yammacin Kogin Yufiretis domin su yardar mini in wuce zuwa Yahuza.