Nehemiah 3:14 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Malkiya ɗan Rekab mai mulkin yankin Bet-Hakkerem ne ya yi gyare-gyaren Ƙofar Juji. Ya sāke gina ta ya kuma sa sakatunta, da sanduna ƙarfenta a wurarensu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مَلْكِيَ طَنْ رٜىٰكَبْ، شُوغَبَنْ عُنْ‌غُوَرْ بٜىٰتْ هَكّٜىٰرٜىٰمْ، يَڠَرَ ڧُواْڢَرْ بُواْلَ؞ يَسَاكٜىٰ غِنَتَ، يَسَا ڧُواْڢُواْڢِنْتَ؞ يَسَا سَكَتَ دَ سَنْدُنَنْ ڧَرْڢٜىٰ نَڟَرٜىٰ ڧُواْڢُواْڢِنْتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Malkiya ɗan Rekab, mai mulkin yankin Bet-akkerem, ya gyara Ƙofar Juji. Ya gina ta, ya sa ƙyamarenta da sandunan ƙarfe na kulle ƙofofinta.