Nehemiah 3:15 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Shallum ɗan Kol-Hoze mai mulkin Mizfa ne ya yi gyare-gyaren Ƙofar Maɓuɓɓuga. Ya sāke gina ta, ya yi mata jinƙa yana sa ƙofofinta, da sakatunta, da kuma sandunan ƙarfenta a wurarensu. Ya kuma gyara katangar tafkin Silowam, ta Lambun Sarki, har zuwa matakalan da suka gangara daga Birnin Dawuda.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
شَلُّمْ طَنْ كُوالْهُواْظٜىٰ، شُوغَبَنْ عُنْ‌غُوَرْ مِظْڢَ، يَڠَرَ ڧُواْڢَرْ عِدُوانْ ضُوَ؞ يَسَاكٜىٰ غِنَتَ، يَرُڢٜىٰتَ؞ يَكُمَسَا ڧُواْڢُواْڢِنْتَ دَ سَكَتَ دَ سَنْدُنَنْ ڧَرْڢٜىٰ نَڟَرٜىٰ ڧُواْڢُواْڢِنْتَ؞ يَكُمَ غِنَا كَتَنْ‌غَرْ تَڢْكِنْ شٜىٰلَ، وَتُواْ سِلُوَمْ، نَغُواْنَرْ سَرْكِے، حَرْ ذُوَا مَتَاكَلَنْ غَنْ‌غَرَ دَغَ بِرْنِنْ دَاوُدَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Shallum ɗan Kolhoze, mai mulkin yankin Mizfa ya gyara Ƙofar Maɓuɓɓuga, ya gina ta, ya rufe ta, ya sa ƙyamarenta, da sandunan ƙarfe na kulle ƙofofinta. Ya kuma gina garun Tafkin Siluwam na gonar sarki, har zuwa matakan da suka gangaro daga Birnin Dawuda.