Nehemiah 3:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Uzziyel ɗan Harhahiya, ɗaya daga cikin masu ƙeran zinariya ne ya yi gyare-gyaren sashe na biye; sai Hananiya, ɗaya daga cikin masu yin turare, ya yi gyare-gyaren biye da wannan. Suka gyara Urushalima har zuwa Katanga Mai Faɗi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عُظِّيٜىٰلْ طَنْ هَرْهَيَ، وَنْدَ شِے مَڧٜىٰرِنْ ظِينَارِيَ نٜىٰ، يَڢَارَ ڠَرَنْ كَتَنْغَرْ دَغَ عِنْدَ مُتَنٜىٰنْ دَسُكٜىٰ ڧَرْڧَشِنْ ڠُومْنَ سُكَ ڟَيَ؞ هَنَنِيَ مَيْيِنْ تُرَارٜىٰ يَڢَارَ ڠَرَنْ كَتَنْغَرْ دَغَ عِنْدَ عُظِّيٜىٰلْ يَڟَيَ؞ مُتَنٜىٰنْ سُكَسَاكٜىٰ غِنَا عُرُوشَلِيمَ حَرْ ذُوَا كَتَنْغَ مَيْ ڢَاطِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kusa da su kuma sai Uzziyel ɗan Harhaya, maƙerin zinariya, ya yi gyare-gyare. Kusa da Uzziyel kuma sai Hananiya, ɗaya daga cikin masu yin turare, ya yi gyare-gyare. Suka gyare Urushalima har zuwa Garu Mai Faɗi.