Nehemiah 5:12 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suka ce, “Za mu mayar musu, kuma ba za mu bukaci wani abu daga gare su ba. Za mu yi yadda ka faɗa.” Sai na tattara firistoci na kuma sa manyan gari da shugabanni su yi rantsuwa don su yi abin da suka yi alkawari.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ شُوغَبَنِّنْ سُكَ أَمْسَ سُكَثٜىٰ «ذَامُيِ كَمَرْ يَدَّ كَڢَطَا؞ ذَامُ مَيَرْ مُسُ دَ كَايَنْسُ، بَذَامُ كَرْٻِ وَنِ بَاشِ دَغَ غَرٜىٰسُبَ كُمَ؞» سَيْ نَكِرَا ڢِرِسْتُواْثِے، نَسَا شُوغَبَنِّ سُرَنْڟٜىٰ أَغَبَنْ ڢِرِسْتُواْثِے ثٜىٰوَ ذَاسُثِكَ أَلْڧَوَرِنْ دَ سُكَ طَوْكَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan suka ce, “Za mu mayar musu da waɗannan abubuwa, ba kuwa za mu bukaci wani abu a gare su ba. Za mu yi abin da ka faɗa.” Sai na kira firistoci su rantsar da su, cewa za su yi yadda suka alkawarta.