Nehemiah 5:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Na kuma kakkaɓe hannuna, na ce, “Duk wanda ya karya wannan alkawari, haka Allah zai kakkaɓe shi daga gidansa da aikinsa. Allah zai kakkaɓe shi, yă wofintar da shi!” Da jin wannan, sai dukan taron suka ce, “Amin,” suka kuma yabi Ubangiji. Mutane kuwa suka yi kamar yadda suka yi alkawari.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ نَكَكَّٻٜىٰ رِغَاتَ نَثٜىٰ «تَهَكَ بَرِ اللَّهْ يَكَكَّٻٜىٰ دُكْ وَنْدَ بَيْ ثِكَ أَلْڧَوَرِنْسَبَ؞ وَتُواْ، بَرِ اللَّهْ يَكَكَّٻٜىٰ غِدَنْسَ دَ دُكَنْ أَبِنْدَ يَكٜىٰدَشِ، يَبَرْ شِ بَا كُواْمٜىٰ؞» سَيْ دُكَنْ تَارُوانْ جَمَعَرْ سُكَ أَمْسَ سُكَثٜىٰ «أَمِينْ!» سُكَ كُمَ يَبِے يَهْوٜىٰهْ ؞ شُوغَبَنِّنْ كُوَ سُكَ ثِكَ أَلْڧَوَرِنْ دَ سُكَيِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai kuma na kakkaɓe hannuna, na ce, “Duk wanda ya karya wannan alkawari, haka Allah zai kakkaɓe shi daga gidansa da aikinsa. Allah zai kakkaɓe shi, ya wofintar da shi.” Sai dukan taron suka amsa, “Amin, amin.” Suka kuma yabi Ubangiji. Suka kuwa cika alkawarin da suka yi.