Nehemiah 5:14 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ban da haka ma, daga shekara ta ashirin ta Sarki Artazerzes, sa’ad da aka naɗa ni in zama gwamnansu a ƙasar Yahuda, har zuwa shekara ta talatin da biyu na mulkinsa, shekara sha biyu ke nan, ko ni, ko ’yan’uwana, ba wanda ya ci abincin da akan ba wa gwamna.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَنْدَ حَكَمَا تُنْ لُواْكَثِنْ دَ عَكَ نَطَنِ ڠُومْنَنْ ڧَسَرْ يَهُودَ، شٜىٰكَرُ غُواْمَشَا بِيُنْ دَ سُكَ وُثٜىٰ، وَتُواْ دَغَ شٜىٰكَرَا تَعَشِرِنْ تَمُلْكٍ سَرْكِے أَرْتَظٜىٰكْظٜىٰسْ حَرْ ذُوَا شٜىٰكَرَرْسَ تَتَلَتِنْ دَ بِيُ، كُواْ نِے كُواْ یَنْعُوَنَ بَاوَنْدَ يَكَرْٻِ رَبُوانْ عَبِنْثِ إِرِنْ نَڠُومْنَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Tun kuma lokacin da na yi mulkin ƙasar Yahuza, a shekara ta ashirin zuwa shekara ta talatin da biyu ta sarautar sarki Artashate, shekara goma sha biyu ke nan, ni ko 'yan'uwana, ba wanda ya karɓi albashin da akan ba mai mulki.