Nehemiah 5:18 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kowace rana akan shirya mini saniya ɗaya, zaɓaɓɓun tumaki shida da waɗansu kaji, kuma kowace kwana goma akan tanadar da ruwan inabi na kowane iri a yalwace. Duk da haka, ban taɓa nemi a ba ni abincin da akan ba wa gwamna ba, domin wahala ta yi wa jama’a yawa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَا يَدَّ عَكَنْ شِرْيَ مِنِ عَبِنْثِ كُواْوَثٜىٰ رَانَ؞ عَكَنْ يَنْكَ بِجِمِ طَيَ دَ تُمَكِ شِدَ مَڢِے ݣَوْ دَ كُمَ كَجِ مَاسُيَوَ؞ عَكُواْوَثٜىٰ رَانَ غُدَا عَثِكِنْ ݣُونَكِے غُواْمَ، عَكَنْ بَادَ سَابُوانْ ضُوً إِنَبِے عَيَلْوَثٜىٰ؞ عَمَّا دُكْدَهَكَ بَنْ كَرْٻِ رَبُوانْ عَبِنْثِ إِرِنْ نَڠُومْنَبَ، سَبُواْدَ وَهَلَ تَيِ وَمُتَنٜىٰ يَوَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ga abincin da ake shiryawa kowace rana, sa ɗaya, da tumaki shida kyawawa, da kuma kaji. A kowace rana ta goma akan kawo salkunan ruwan inabi masu yawa, amma duk da haka ban karɓi albashin da akan ba mai mulki ba, domin wahala ta yi wa mutane yawa.