Nehemiah 6:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Wata rana na tafi gidan Shemahiya ɗan Delahiya, ɗan Mehetabel, wanda aka hana fita a gidansa. Ya ce mini, “Mu sadu gobe a gidan Allah, a cikin haikali, mu kuma kulle ƙofofin haikali, gama mutane suna zuwa su kashe ka, tabbatacce za su zo da dare su kashe ka.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَتَرَانَ نَظِيَرْثِ شٜىٰمَيَ طَنْ دٜىٰلَيَ، وَتُواْ جِيكَنْ مٜىٰهٜىٰتَبٜىٰلْ، أَغِدَنْسَ؞ شٜىٰمَيَ كُوَ بَيْ عِيَ ڢِتَ دَغَ غِدَنْسَبَ؞ يَثٜىٰ مِنِ «بَرِ مُتَڢِے مُٻُيَ أَ غِدَنْ اللَّهْ ، ثِكِنْ وُرِے مَيْ ڟَرْكِے أَ هَيْكَلِ، مُكُمَ كُلّٜىٰ ڧُواْڢُواْڢِنْ، دُواْمِنْ سُنَ ذُوَا سُكَشٜىٰكَ؞ لَلَّيْ سُنَ ذُوَا سُكَشٜىٰكَ دَ دَرٜىٰ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da na ziyarci Shemaiya ɗan Delaiya, wato jikan wanda aka hana shi fita, sai ya ce mini, “Bari mu tafi cikin Haikalin Allah, mu rufe ƙofofin Haikalin, gama suna zuwa su kashe ka, za su iya zuwa a wani dare su kashe ka.”