Nehemiah 8:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan Nehemiya gwamna, Ezra firist da kuma wanda yake malamin Doka, da Lawiyawa waɗanda suke koyar da mutane, suka ce musu duka, “Wannan rana mai tsarki ce ga Ubangiji Allahnku. Kada ku yi makoki ko kuka.” Gama dukan mutane suna ta kuka yayinda suke sauraran kalmomin Dokar.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ مُتَنٜىٰ سُكٜىٰ جِنْ أَبِنْدَ عَكٜىٰ كَرَنْتَاوَا دَغَ لِتَّڢِنْ كُواْيَرْوَرْ مُوسَٰى، سَيْ سُكَيِ تَكُوكَا؞ سَيْ نٜىٰهٜىٰمِيَ مَيْ مُلْكِ دَ عُزَيْرُ ڢِرِسْتِ وَنْدَ شِے مَلَمِنْ كُواْيَرْوَا نٜىٰ دَ كُمَ لَوِيَاوَنْ دَسُكٜىٰيِ وَجَمَعَرْ ڢَسَّرَ سُكَثٜىٰ وَدُكَنْسُ «وَنَّنْ رَانَثٜىٰ دَ عَكَكٜىٰٻٜىٰ دَ ڟَرْكِے غَ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْكُ، سَبُواْدَ حَكَ كَدَ كُيِ بَڧِنْ ثِكِ كُواْ كُوكَا؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Nehemiya kuwa wanda yake mai mulki, da Ezra, firist da magatakarda, da Lawiyawa waɗanda suka fassara wa jama'a dokokin, suka ce wa dukan jama'a, “Wannan rana tsattsarka ce, ta Ubangiji Allahnku, kada ku yi baƙin ciki ko kuka.” Gama mutane duka sai kuka suke sa'ad da aka karanta musu dokokin.