Nehemiah 9:25 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suka kame birane masu katanga masu ƙarfi, da ƙasa masu ba da amfani; suka mallaki gidaje cike da kowane irin abu mai kyau, da rijiyoyin da aka riga aka haƙa, da gonakin inabi, da gonakin itatuwan zaitun da kuma itatuwan ba da ’ya’ya a yalwace a ciki. Suka ci suka ƙoshi, suka kuma yi ƙiba; suka ji daɗi cikin alherinka mai girma.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُتَنٜىٰنْكَ سُكَ ڨُوثٜىٰ بِرَنٜىٰ مَاسُ كَتَنْغَ دَ ڧَسَا مَيْ يَوَنْ أَمْڢَانِ؞ سُكَ ڨُوثٜىٰ غِدَاجٜىٰ ثِكٜىٰ دَ كَايَ مَاسُ ݣَوْ إِرِ إِرِ، دَ رِجِيُواْيِنْ دَ أَنْرِغَا أَنْتُواْنَ، دَ عِتَتُوَنْ إِنَبِے دَ عِتَتُوَنْ ظَيْتُنْ، دَ عِتَتُوَ دَيَوَ مَاسُ یَیَ؞ سُكَثِ، سُكَ ڧُواْشِ، سُكَيِ ڧِبَ، سُكَجِ دَاطِنْ أَلْحٜىٰرِنْدَ كَيِ مُسُ عَيَلْوَثٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sun ci birane masu garu, da ƙasa mai dausayi, Da gidaje cike da dukiya, da rijiyoyi, da gonakin inabi, Da itatuwan zaitun, da itatuwa masu 'ya'ya. Suka ci dukan abin da suke so, suka yi taiɓa, Suka mori dukan kyawawan abubuwan da ka ba su.