Nehemiah 9:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A kan dakalin kuwa akwai Lawiyawa, wato, Yeshuwa, Bani, Kadmiyel, Shebaniya, Bunni, Sherebiya, Bani da Kenani tsaye, waɗanda suka kira da babbar murya ga Ubangiji Allahnsu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
لَوِيَاوَا سُكَ ڟَيَ عَكَنْ مَتَاكَلَنْ بَبَّنْ تٜىٰبُرِنْ دَ عَكَيِ دُواْمِنْسُ؞ عَثِكِنْسُ كُوَ أَݣَويْ يٜىٰشُوَ دَ بَنِ دَ كَدْمِيٜىٰلْ دَ شٜىٰبَنِيَ دَ بُنِّ دَ شٜىٰرٜىٰبِيَ دَ بَنِ دَ كٜىٰنَنِ؞ وَطَنَّنْ سُكَيِ أَدُّعَ دَ بَبَّرْ مُرْيَ ذُوَاغَ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Yeshuwa, da Bani, da Kadmiyel, da Shebaniya, da Bunni, da Sherebiya, da Bani, da Kenani suka tsaya a kan dakalin Lawiyawa, suka ta da murya da ƙarfi ga Ubangiji Allahnsu.