Numbers 10:25 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A ƙarshe, a matsayi masu gadin bayan dukan ɓangarori, sai ɓangaren sansanin Dan suka tashi bisa ga ƙa’idar da aka yi, aka kuma umarta. Ahiyezer ɗan Ammishaddai ne shugaba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَڧَرْشٜىٰ، سَيْ تُوتَرْ ذُرِيَرْ دَنْ تَوُثٜىٰ غَبَ تَكَامَ حَنْيَ، مُتَنٜىٰنْ دَنْ كُمَ سُكَ ڢِتَ ڧُنْ‌غِيَ ڧُنْ‌غِيَ، سُنَ رُڢٜىٰ بَايَنْ دُكَنْ سَوْرَنْ ظُرِيُواْيِ؞ أَهِيٜىٰظٜىٰرْ طَنْ أَمِّشَدَّيْ، شِينٜىٰ شُوغَبَنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A ƙarshe sai ƙungiyar mutanen Dan da take bayan dukan zangon, ta tashi, ƙungiyoyinsu suna biye. Shugaban rundunarsu Ahiyezer ne, ɗan Ammishaddai.