Numbers 10:35 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Duk kuma sa’ad da akwatin ya kama hanya, sai Musa ya ce, “Ka tashi, ya Ubangiji! Ka sa maƙiyanka su warwatse; masu ƙinka kuma su gudu a gabanka.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكْ لُواْكَثِنْ دَ عَݣُوتِنْ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَ يَتَاشِ يَكَامَ حَنْيَ، سَيْ مُوسَٰى يَثٜىٰ، « يَهْوٜىٰهْ ، بَرِ كَتَاشِ! بَرِ كَوَاڟَرْدَ أَبُواْكَنْ غَابَنْكَ، بَرِ مَاسُ ڧِنْكَ سُغُدُ دَغَ غَرٜىٰكَ!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Duk kuma lokacin da akwatin zai tashi, sai Musa ya ce, “Ka tashi, ya Ubangiji, ka sa maƙiyanka su warwatse, ka sa waɗanda suke ƙinka su gudu gabanka.”