Numbers 11:12 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ni ne na yi cikin dukan mutanen nan? Ni ne na haife su? To, me ya sa ka ce in ɗauke su a ƙirjina kamar yadda mai reno yake rungume jariri, zuwa ƙasa wadda ka yi alkawari da rantsuwa za ka ba wa kakanninsu?
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نِے نَا طَوْكِ ثِكِنْسُ نٜىٰ؟ كُواْ نِے نَا حَيْڢٜىٰسُنٜىٰ؟ دُوانْمٜىٰ ذَاكَثٜىٰ مِنِ إِنْ طَوْكِ وَطَنَّنْ مُتَنٜىٰ كَمَرْ يَدَّ مَيْ رٜىٰنُواْ تَكَنْ طَوْكِ طَنْ جَرِرِ عَڧِرْجِنْتَ، حَرْ ذُوَا ڧَسَرْ دَكَيْ كَا ضَنْڟٜىٰ وَكَاكَنِّنْسُ ثٜىٰوَ ذَاكَ بَاسُ؟
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ni na ɗauki cikinsu? Ko kuwa ni ne na haife su, har da za ka ce mini, ‘Ka ɗauke su a ƙirjinka, kamar yadda mai reno yake rungume jariri, zuwa ƙasa wadda ka rantse za ka bai wa kakanninsu?’