Numbers 11:18 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ka gaya wa mutane, ‘Ku tsarkake kanku don gobe, za ku ci nama. Ubangiji ya ji ku sa’ad da kuka yi kuka cewa, “Da mun sami nama mun ci mana! Ai, da ba mu da damuwa, gama lokacin da muke zama cikin Masar ba mu da damuwa!” Yanzu Ubangiji zai ba ku nama, za ku kuma ci.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«ڢَطَا وَمُتَنٜىٰنْ ثٜىٰوَ سُكٜىٰٻٜىٰ كَنْسُ دَ ڟَرْكِے دُواْمِنْ غُواْبٜىٰ، ذَاسُ كُوَثِ نَامَ؞ يَهْوٜىٰهْ ذَيْبَاسُ نَامَ، تُنْدَ سُكَيِ غُنَغُنِ، يَكُمَ جِيسُ دَ سُكَثٜىٰ، ‹دَمَا مُسَامِ نَامَ مُثِ! حَڧِيڧَ يَڢِ مَنَ ݣَوْ عَڧَسَرْ مَصَرْ!› سَبُواْدَ حَكَ ذَاسُثِ نَامَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ka ce wa jama'ar, su tsarkake kansu don gobe, za su ci nama, gama Ubangiji ya ji gunagunin da suka yi, da suka ce, ‘Wa zai ba mu nama mu ci? Ai, zama cikin Masar ya fi mana.’ Domin haka Ubangiji zai ba su nama, za su kuwa ci.