Numbers 12:10 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da girgijen ya tashi daga bisa Tentin, sai ga Miriyam tsaye, kuturwa, fari fat. Haruna kuwa ya juya wajenta ya ga ta kuturce;
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ ڧُنْشِنْ غِرْغِجٜىٰنْ يَتَاشِ دَغَ بِسَ تٜىٰنْتِنْ، سَيْغَا مَرْيَمُ أَڟَيٜىٰ دَ ثُوتَرْ ڢَتَرْ جِكِے، تَايِ ڢَرِ ڢَتْ كَمَرْ أَوْدُغَ؞ دَ هَٰرُونَ يَجُويَ يَكَلّٜىٰتَ، سَيْ يَغَ تَا سَامِ ثُوتَرْ ڢَتَرْ جِكِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da al'amudin girgijen ya tashi daga kan alfarwar, sai ga Maryamu ta kuturce, fari fat kamar auduga. Da Haruna ya juya wajen Maryamu, ya ga ta zama kuturwa.