Numbers 13:32 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai suka yaɗa labari marar kyau ga Isra’ilawa game da ƙasar da suka binciko. Suka ce, “Ƙasar da muka ratsa cikinta domin mu leƙi asirinta, tana cinye waɗanda suke zama a cikinta. Dukan mutanen da muka gani a wurin, ƙatti ne.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ سُكَ بَظَ مُوغُنْ رَهُواْتُواْ وَجَمَعَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ غَمٜىٰدَ ڧَسَرْدَ سُكَ لٜىٰڧِ أَسِيرِنْتَ؞ سُكَثٜىٰ «ڧَسَرْ دَ مُكَ تَڢِے مُكَ بِنْثِكَ، إِنْ مُتُمْ يَشِغَ دَ وُيَ يَڢِتَ دَ رَيْ، غَمَا دُكَنْ مُتَنٜىٰنْ دَ مُكَ غَنِ أَوُرِنْ ڧَتِّ نٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Haka suka kawo wa 'yan'uwansu, Isra'ilawa, mugun rahoton ƙasa wadda suka leƙi asirinta, suka ƙara da cewa, “Ƙasar da muka ratsa cikinta domin mu leƙi asirinta, tana cinye waɗanda suke zaune a cikinta, dukan mutane kuma da muka gani a cikinta ƙatti ne.