Numbers 14:35 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ni, Ubangiji na faɗa, zan kuwa aikata waɗannan abubuwa a kan dukan muguwar jama’an nan da suka haɗa kai, suka tayar mini. Za su sadu da ƙarshensu a wannan hamada; a nan za su mutu.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نِے يَهْوٜىٰهْ نَا ڢَطَا؞ حَڧِيڧَ ذَنْيِ حَكَ عَكَنْكُ، كُو مُوغُنْ تَارُوانْ جَمَعَرْ دَ كُكَ حَطَ بَاكِ عَكَيْنَ؞ أَ دَاجِنَّنْ نٜىٰ ذَاكُ ڧَارٜىٰ كَكَڢْ، كُواْوَنٜىٰ طَيَنْكُ ذَيْ مُتُ؞› »
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ni Ubangiji na faɗa, hakika, haka zan yi da wannan mugun taron jama'ar da suka haɗa kai, suka tayar mini. Za su ƙare ƙaƙaf a wannan jeji, a nan za su mutu.’ ”