Numbers 15:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
sai shi wanda ya kawo hadayar yă miƙa wa Ubangiji hadaya ta gari mai laushi mai kyau, kashi ɗaya bisa goma na efa wanda aka kwaɓa da kwalaba ɗaya na mai.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكْ وَنْدَ ذَيْ مِيڧَ إِرِنْ وَنَّنْ هَدَايَ غَ يَهْوٜىٰهْ ، ذَيْ كُمَ كَٰوُاْ هَدَايَ تَهَڟِ؞ هَدَايَ تَهَڟِ ذَاتَ ذَمَ تَكِلُواْ طَيَ نَغَارِنْ حَڟِ مَيْ لَوْشِ، وَنْدَ عَكَ ݣُوٻَ دَ لِتَ طَيَ نَمَنْ ظَيْتُنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
sai shi wanda ya kawo hadayar ga Ubangiji, ya kuma kawo hadaya ta gari, humushin garwa guda kwaɓaɓɓe da rubu'in moɗa na mai.