Numbers 16:40 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
yadda Ubangiji ya umarce shi, ta wurin Musa. Wannan ya zama abin tuni ga Isra’ilawa domin kada wani da ba firist ba, bai kuwa fito a cikin zuriyar Haruna ba, yă zo don yă ƙona turare a gaban Ubangiji, domin kada yă zama kamar Kora da mabiyansa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَنَّنْ يَذَمَ أَبِنْ غَرْغَطِے غَ إِسْرَٰٓءِيلَاوَا ثٜىٰوَ كَدَ وَنْدَ بَ ڢِرِسْتِ بَ، وَتُواْ وَنْدَ بَدَغَ ذُرِيَرْ هَٰرُونَ بَ، يَيِ كُسَدَ بَغَدٜىٰنْ دُواْمِنْ يَڧُواْنَ تُرَارٜىٰ أَغَبَنْ يَهْوٜىٰهْ ؞ دُكْ وَنْدَ بَ ڢِرِسْتِ بَايَ كُمَيِ كُسَدَ بَغَدٜىٰنْ دُواْمِنْ يَڧُواْنَ تُرَارٜىٰ، أَبِنْدَ يَڢَرُ دَ ڧَارُونَ ذَيْسَامٜىٰشِ؞ أَنْيِ حَكَ بِسَغَ يَدَّ يَهْوٜىٰهْ يَڢَطَا وَ عٜىٰلٜىٰيَظَرْ تَبَاكِنْ مُوسَٰى؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Zai zama abin tunawa ga Isra'ilawa domin kada wanda ba firist ba, ba kuwa a cikin zuriyar Haruna ba, ya guso don ya ƙona turare a gaban Ubangiji, domin kada ya zama kamar Kora da ƙungiyarsa. Haka Ubangiji ya faɗa wa Ele'azara ta bakin Musa.