Numbers 16:46 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Musa ya ce wa Haruna, “Ka ɗauki farantinka ka sa turare a ciki, da wuta daga bagade, ka yi maza ka tafi wajen taron, ka yi kafara dominsu. Gama fushin Ubangiji ya riga ya sauko; an kuma fara annoba.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ مُوسَٰى يَثٜىٰ وَ هَٰرُونَ «طَوْكِ ݣُونُوانْكَ نَڧُواْنَ تُرَارٜىٰ، كَسَا غَرْوَشِنْ وُتَادَغَ بَغَدٜىٰنْ عَكَيْ، كَكُمَسَا تُرَارٜىٰ عَكَنْ غَرْوَشِنْ؞ سَيْ كَتَڢِے دَ سَوْرِ ذُوَا وُرِنْ جَمَعَ، كَيِ ڧَٰعِدَ تَطَوْكَرْ أَلْحَكِنْ ذُنُوبِنْسُ؞ يِسَوْرِ! غَمَا ڢُشِنْ يَهْوٜىٰهْ يَا رِغَا يَا ٻَرْكٜىٰ، كُمَ بَلَعِ يَا رِغَا يَا ڢَارَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan Musa ya ce wa Haruna, “Ɗauki farantin turare, ka cika shi da wuta daga bagade, ka zuba turaren wuta a ciki, ka tafi da sauri wurin taron, ka yi kafara dominsu, gama fushin Ubangiji ya riga ya sauko, an fara annoba.”