Numbers 18:19 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kome da aka keɓe daga tsarkakakku hadayun da Isra’ilawa suka miƙa wa Ubangiji, na ba ka, da kai da ’ya’yanka maza da mata a matsayin zaunannen rabo. Wannan madawwamin alkawarin gishiri ne a gaban Ubangiji dominka da zuriyarka.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«دَغَ ثِكِنْ دُكَنْ بَيٜىٰ بَيٜىٰ مَاسُ ڟَرْكِے وَطَنْدَ إِسْرَٰٓءِيلَاوَا سُكَ مِيڧَ مِنِ، رَبُوانْكَ نٜىٰ نَبَاكَ، دَكَيْ دَ یَیَنْكَ مَظَا دَ مَاتَا؞ وَنَّنْ رَبُوانْكَنٜىٰ نَدِنْدِنْدِنْ؞ وَنَّنْ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَ تَغِشِرِ تَهَرْ أَبَدَاثٜىٰ أَغَبَنْ يَهْوٜىٰهْ دُواْمِنْكَ دَ ذُرِيَرْكَ، غَمَا غِشِرِ عَلَمَثٜىٰ تَيَرْجٜىٰجٜىٰنِيَ دَ اللَّهْ نْكُ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Duk hadayu na ɗagawa na tsarkakakkun abubuwan da Isra'ilawa suka miƙa wa Ubangiji, na ba ka, da kai da 'ya'yanka mata da maza a kowane lokaci. Wannan alkawarin gishiri ne na Ubangiji dominka da zuriyarka.”