Numbers 19:20 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma in wanda yake da ƙazanta bai tsarkake kansa ba, dole a ware shi daga cikin jama’a, domin ya ƙazantar da wuri mai tsarki na Ubangiji. Ba a yayyafa masa ruwa na tsarkakewa ba, ya zama da ƙazanta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«دُكْ وَنْدَ يَڧَظَنْتُ يَكُمَڧِ يَڟَبْتَثٜىٰ كَنْسَ دَ وَنَّنْ ضُوً ڟَبْتَثٜىٰوَ ذَيْ كَسَنْثٜىٰ مَيْ ڧَظَنْتَا، كُمَ ذَاعَ كَوَرْ دَشِ دَغَ تَارُوانْ جَمَعَ، غَمَا يَا ڧَظَنْتَرْدَ وُرِے مَيْ ڟَرْكِے نَ يَهْوٜىٰهْ ؞ ذَيْ كَسَنْثٜىٰ مَيْ ڧَظَنْتَا، تُنْدَيَكٜىٰ بَعَيَيَّڢَا مَسَ ضُوَ مَيْ ڟَبْتَثٜىٰوَبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Amma mutumin da ba shi da tsarki, bai kuwa tsarkake kansa ba, ba za a lasafta shi cikin jama'ar Allah ba, tun da yake ya ƙazantar da alfarwa ta sujada ta Ubangiji, gama ba a yayyafa masa ruwan da akan yayyafa wa marasa tsarki ba.