Numbers 2:10 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A kudu, a nan ne sashe sansanin mutanen Ruben a ƙarƙashin ƙa’idarsu, za su yi sansani. Shugaban mutanen Ruben shi ne Elizur ɗan Shedeyur.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَطَنْدَ ذَاسُ كَڢَ تٜىٰنْتُنَنْسُ أَغٜىٰڢٜىٰنْ كُدُ، سُونٜىٰ ذُرِيَرْ رَعُبَيْنُ عَڧَرْڧَشِنْ تُوتَرْسُ، بِسَغَ ڧُنْ‌غِيَ ڧُنْ‌غِيَرْسُ؞ شُوغَبَنْ ذُرِيَرْ رَعُبَيْنُ شِينٜىٰ عٜىٰلِظُرْ طَنْ شٜىٰدٜىٰيُرْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ƙungiyoyin kabilar Ra'ubainu za su sauka su kafa tutarsu a sashin kudu a ƙarƙashin jagorancin shugabanninsu, kamar haka, Kabila Shugaba Jimilla Ra'ubainu Elizur ɗan Shedeyur 46,500 Saminu Shelumiyel ɗan Zurishaddai 59,300 Gad Eliyasaf ɗan Deyuwel 45,650 Jimilla duka, 151,450) duba ɗari da hamsin da ɗaya, da ɗari huɗu da hamsin. Ƙungiyoyin kabilar Ra'ubainu za su bi bayan na Yahuza.