Numbers 20:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Waɗannan su ne ruwan Meriba, inda Isra’ilawa suka yi wa Ubangiji gunaguni, inda kuma ya nuna kansa mai tsarki a cikinsu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَنْكِرَا وُرِنْ ضُوًنَنْ دَ سُونَ مٜىٰرِبَ، سَبُواْدَ أَوُرِنْ نٜىٰ جَمَعَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ سُكَيِ وَ يَهْوٜىٰهْ غُنَغُنِ؞ أَ نَنْ كَدٜىٰشْ كُمَ يَهْوٜىٰهْ يَنُونَ مُسُ لَلَّيْ شِے مَيْ ڟَرْكِے نٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Wannan ya faru ne a Meriba inda mutanen Isra'ila suka yi wa Ubangiji gunaguni, inda shi kuma ya nuna musu shi mai tsarki ne.