Numbers 21:22 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ka bari mu ratsa ta ƙasarka. Ba za mu shiga wata gona ba, ba za mu kuma shiga gonar inabi, ko mu sha ruwa daga wata rijiya ba. Za mu bi ta babbar hanyar sarki, har mu fita ƙasarka.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«رَنْكَيَدَطٜىٰ! كَيَرْدَ مَنَ مُبِے تَڧَسَرْكَ؞ بَذَامُبِے تَثِكِنْ غُواْنَكِنْكَبَ، كُواْ غُواْنَكِنْ إِنَبِنْكَبَ؞ بَذَامُ شَا ضُوَ دَغَ وَتَ رِجِيَرْكَبَ؞ ذَامُبِے تَهَنْيَرْ سَرْكِے كَوَيْ، حَرْ مُڢِتَ دَغَ يَنْكِنْكَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Ka yarda mana mu ratsa ta ƙasarka, ba za mu ratsa ta cikin gonaki, ko cikin gonakin inabi ba, ba kuwa za mu sha ruwan rijiyarka ba, gwadaben sarki za mu bi sosai, har mu fita daga karkararka.”