Numbers 21:26 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sihon sarkin Amoriyawa ya yi mulkin Heshbon, bayan ya ci sarkin Mowab na dā da yaƙi, ya kuma ƙwace dukan ƙasarsa har zuwa arewancin kogin Arnon.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَمَا هٜىٰشْبُوانْ بَبَّنْ بِرْنِنْ سَرْكِے سِهُوانْ نَ أَمُواْرِيَاوَا نٜىٰ؞ وَنَّنْ سَرْكِے سِهُوانْ شِينٜىٰ يَيِ يَاڧِ دَ سَرْكِنْ مُواْوَبْ نَدَا، يَكُمَ ڨُوثٜىٰ دُكَنْ ڧَسَرْسَ حَرْ ذُوَا كُواْغِنْ أَرْنُوانْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Gama Heshbon ita ce birnin Sihon,Sarkin Amoriyawa, wanda ya yi yaƙi da Sarkin Mowab na dā. Ya ƙwace ƙasarsa duka daga hannunsa har zuwa Kogin Arnon.