Numbers 21:29 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kaitonki, Mowab! Gunkinki Kemosh ya yashe mutanenki; aka kuma kama su, aka kai su bauta wajen Sihon sarkin Amoriyawa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«كَيْتُوانْكُ، يَا مُتَنٜىٰنْ مُواْوَبْ! تَاكُتَاڧَارٜىٰ، يَا كُو مُتَنٜىٰنْ غُنْكِنْ كٜىٰمُواشْ! يَمَيْدَ یَیَنْسَ یَنْ غُدُنْ ڟِيرَا، یَیَنْسَ مَاتَا مَا، وَطَنْدَ عَكَ ڨُوثٜىٰ دَ يَاڧِ تَهَنُّنْ سَرْكِے سِهُوانْ نَ أَمُواْرِيَاوَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kaitonku, ku mutanen Mowab! Ku masu sujada ga Kemosh kun lalace! Gumakanku sun sa mutane su zama 'yan gudun hijira, Mata kuwa, Sihon, Sarkin Amoriyawa ya kama su.