Numbers 22:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kashegari Bala’am ya tashi ya ce wa dattawan Balak, “Ku koma ƙasarku, domin Ubangiji ya hana ni in tafi tare da ku.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَشٜىٰغَرِ دَ سَڢٜىٰ سَيْ بَلَعَمْ يَتَاشِ يَجٜىٰ وُرِنْ دَتَّاوَنْ سَرْكِے بَلَكْ يَثٜىٰ مُسُ «كُكُواْمَ ڧَسَرْكُ، غَمَا يَهْوٜىٰهْ بَيْ يَرْدَ مِنِ إِنْ تَڢِے تَرٜىٰدَكُوبَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da safe Bal'amu ya tashi, ya ce wa dattawan Balak, “Ku koma ƙasarku, gama Ubangiji bai yarda mini in tafi tare da ku ba.”