Numbers 22:31 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan Ubangiji ya buɗe idanun Bala’am, ya kuwa ga mala’ikan Ubangiji tsaye a hanya da takobi a zāre. Sai ya sunkuyar da kansa, ya fāɗi rubda ciki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً يَهْوٜىٰهْ يَبُوطٜىٰ إِدَانُنْ بَلَعَمْ، يَكُمَ غَا مَلاَىِٕكَنْ يَهْوٜىٰهْ يَنَ ڟَيٜىٰ أَ حَنْيَ دَ تَكُواْبِے أَ ذَارٜىٰ أَ حَنُّنْسَ؞ سَيْ بَلَعَمْ يَرُسُنَ يَڢَاطِ دَ ڢُسْكَرْسَ حَرْ ڧَسَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji kuwa ya buɗe idanun Bal'amu, ya ga mala'ikan Ubangiji yana tsaye a hanya da takobi zāre a hannunsa. Sai ya sunkuyar da kansa, ya fāɗi rubda ciki.