Numbers 22:35 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Mala’ikan Ubangiji ya ce wa Bala’am, “Ka tafi tare da mutanen, amma abin da na faɗa maka ne kaɗai za ka faɗa.” Saboda haka Bala’am ya tafi tare da dattawan Balak.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مَلاَىِٕكَنْ يَهْوٜىٰهْ كُوَ يَثٜىٰ وَ بَلَعَمْ «تَڢِے تَرٜىٰدَ مُتَنٜىٰنْ، عَمَّا أَبِنْدَ نَڢَطَا مَكَ كَطَيْ نٜىٰ ذَاكَ ڢَطَا؞» سَيْ بَلَعَمْ يَتَڢِے تَرٜىٰدَ دَتَّاوَنْ سَرْكِے بَلَكْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji kuwa ya ce wa Bal'amu, “Tafi tare da mutanen, amma abin da na faɗa maka shi kaɗai za ka faɗa.” Sai Bal'amu ya tafi tare da dattawan Balak.