Numbers 23:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka ya tafi ya same Balak tsaye a kusa da hadayarsa, tare da dattawan Mowab. Balak ya tambaye Bala’am ya ce, “Mene ne Ubangiji ya ce?”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ يَكُواْمَ وُرِنْ سَرْكِے بَلَكْ، يَسَامٜىٰشِ أَڟَيٜىٰ كُسَدَ هَدَايَرْسَ تَڧُواْنَاوَا تَرٜىٰدَ دُكَنْ دَتَّاوَنْ مُواْوَبْ؞ سَرْكِے بَلَكْ كُوَ يَثٜىٰ مَسَ «مٜىٰ يَهْوٜىٰهْ يَڢَطَا؟»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Bal'amu ya koma wurin Balak ya same shi yana tsaye kusa da hadayarsa ta ƙonawa tare da dattawan Mowab. Balak kuwa ya ce masa, “Me Ubangiji ya faɗa?”