Numbers 24:16 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
maganar mutumin da ya saurari maganar Allah, wanda yake da sani daga Mafi Ɗaukaka, wanda yake ganin wahayi daga Maɗaukaki, wanda ya fāɗi rubda ciki, wanda kuma idanunsa suna a buɗe.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَنَّبْثِ نَمَيْ جِنْ كَلْمُواْمِنْ اللَّهْ ، مُتُمِنْدَ يَكَرْٻِ سَنِ دَغَ مَڢِے طَوْكَكَ ، مَيْ غَنِنْ رُعُيَ دَغَ مَيْ إِيكُواْ دُكَ ، مَيْ كَرْٻَرْ سَڧُواْ دَغَ اللَّهْ ، وَنْدَ عَكَ بُوطٜىٰمَسَ عِدُواْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Faɗar wanda yake jin faɗar Allah, Wanda ya san hikimar Maɗaukaki, Wanda yake ganin wahayin Mai Iko Dukka, Yana durƙurshe, amma idanunsa a buɗe suke.