Numbers 24:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Allah ya fitar da su daga Masar; suna da ƙarfin kutunkun ɓauna. Sun cinye abokan gāban, suka kakkarya ƙasusuwansu; da kibiyoyinsu suka sossoke su.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
اللَّهْ وَنْدَ يَڢِتَرْ دَسُو دَغَ مَصَرْ، ڧَرْڢِنْسَ كَمَرْ نَڧَهُوانْ ٻَوْنَ نٜىٰ دُواْمِنْسُ؞ يَعْڧُوبَ ذَيْثِنْيٜىٰ أَلْعُمَّيْ مَاسُ ڧِنْسَ، يَكَكَّرْيَ ڧَسُسُوَنْسُ، يَسُواْسُّواْكٜىٰسُ دَ كِبِيُواْيِنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Allah ne ya fisshe su daga Masar, Kamar kutunkun ɓauna yake a gare su, Yakubu zai cinye maƙiyansa, Zai kakkarya ƙasusuwansu, ya mummurɗe kibansu.