Numbers 27:11 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
In mahaifinsa ba shi da ’yan’uwa, a ba da gādonsa ga danginsa na kusa, a kabilarsa don yă mallaka. Wannan ya zama ƙa’ida wa Isra’ilawa, yadda Ubangiji ya umarci Musa.’ ”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عِدَنْ كُمَ بَابَنْسَ بَاشِدَ یَنْعُوَ، سَيْ كَبَا مُتُمْ مَڢِے كُسَ ثِكِنْ دَنْ‌غِنْسَ غَادُوانْسَ؞ وَنَّنْ ذَيْ ذَمَ ڧَٰعِدَ دَ عُمَرْنِ غَ إِسْرَٰٓءِيلَاوَا، بِسَغَ يَدَّ نِے يَهْوٜىٰهْ نَعُمَرْثٜىٰكَ؞› »
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Idan kuma ba shi da su, sai a ba danginsa na kusa su mallaka, wannan zai zama umarni da ka'ida ga Isra'ilawa kamar yadda ni, Ubangiji na umarce ka.’ ”