Numbers 28:14 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da kowane bijimi, za a kasance da hadaya ta sha, na rabin kwalabar ruwan inabi; da rago kuwa, a kasance da kashi ɗaya bisa uku; da kowace tunkiya kuma, a kasance da kashi ɗaya bisa huɗu. Wannan ita ce hadaya ta ƙonawa don tsayawar kowane sabon wata na shekara.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
هَدَايَرْسُ تَأَبِنْ شَا كُوَ ذَاتَ كَسَنْثٜىٰ حَكَ، لِتَ بِيُ نَضُوً إِنَبِے دُواْمِنْ كُواْوَنٜىٰ بِجِمِ دَ لِتَ طَيَ دَ رَبِے دُواْمِنْ كُواْوَنٜىٰ ضَغُواْ دَ لِتَ طَيَ دُواْمِنْ كُواْوَنٜىٰ طَنْ ضَغُواْ؞ وَنَّنْ ڧَٰعِدَ ثٜىٰ تَهَدَايَ تَڧُواْنَاوَا دُواْمِنْ كُواْوَنٜىٰ سَابُوانْ وَتَ أَ شٜىٰكَرَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Hadaya ta sha kuwa za ta zama rabin moɗa na ruwan inabi don kowane bijimi, sulusin moɗa kuma don kowane rago, rubu'in moɗa don kowane ɗan rago. Wannan ita ce ka'idar hadaya ta ƙonawa don tsayawar kowane wata na shekara.