Numbers 29:13 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A miƙa hadayar da aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, hadaya ta ƙonawa ta bijimai guda sha uku, raguna biyu, da ’yan raguna goma sha huɗu, bana ɗaya-ɗaya, dukansu marasa lahani.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَاكُ مِيڧَ هَدَايَ تَڧُواْنَاوَا، هَدَايَرْدَ عَكَ مِيڧَ دَ وُتَا، مَيْ دَاطِنْ ڧَنْشِ غَ يَهْوٜىٰهْ دَ یَنْ بِجِمَيْ غُواْمَشَا عُكُ دَ رَغُنَ بِيُ دَ یَنْ رَغُنَ غُواْمَشَا حُطُ مَاسُ شٜىٰكَرَا طَيَ طَيَ؞ دَبُّواْبِنْ ذَاسُ ذَمَ مَرَسَ تَبُواْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da 'yan bijimai goma sha uku, da raguna biyu, da 'yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Dabbobin nan su zama marasa lahani.