Numbers 3:13 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
gama duk ’ya’yan fari nawa ne. Lokacin da karkashe duk ’ya’yan fari a Masar, na keɓe wa kaina kowane ɗan fari a Isra’ila, ko mutum, ko dabba. Za su zama nawa. Ni ne Ubangiji.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَمَا دُكَنْ یَیَنْ ڢَارِ نَوَنٜىٰ؞ لُواْكَثِنْدَ نَكَشٜىٰ دُكَنْ یَیَنْ ڢَارِ نَڧَسَرْ مَصَرْ، نَكٜىٰٻٜىٰوَ كَيْنَ دُكَنْ یَیَنْ ڢَارِ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ، كُواْ نَمُتُمْ كُواْ نَدَبَّ؞ ذَاسُ ذَمَ نَوَ؞ نِنٜىٰ يَهْوٜىٰهْ ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Gama 'yan fari duka nawa ne, tun daga ranar da na kashe 'ya'yan fari na ƙasar Masar, na keɓe wa kaina duk ɗan fari na Isra'ila, na mutum da na dabba. Za su zama nawa, ni ne Ubangiji.”