Numbers 3:38 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Musa da Haruna da ’ya’yansu za su yi sansani gabas da tabanakul, wajen fitowar rana; a gaban Tentin Sujada. Su ne da hakkin lura da wuri mai tsarki a madadin Isra’ilawa. Duk wani wanda ba ya wannan aiki, ya kuma kusaci wuri mai tsarki, za a kashe shi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُوسَٰى دَ هَٰرُونَ دَ یَیَ مَظَا نَ هَٰرُونَ ذَاسُ كَڢَ تٜىٰنْتُنَنْسُ أَغَبَنْ تٜىٰنْتِنْ، عَتَغَبَسْ دَ تٜىٰنْتِنْ سَدُوَ وَجٜىٰنْ ڢِتُواْوَرْ رَانَ؞ سُونٜىٰ سُنَدَ حَكِّنْ عَيْكِ عَثِكِنْ وُرِے مَيْ ڟَرْكِے دَ كُواْوَنٜىٰ إِرِنْ عَيْكِنْ دَ ذَاعَيِ دُواْمِنْ إِسْرَٰٓءِيلَاوَا؞ عِدَنْ وَنِ مُتُمْ دَبَمْ يَيِ ڧُواْڧَرِنْ يِنْ وَنَّنْ عَيْكِ، ذَاعَ كَشٜىٰشِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Waɗanda za su yi zango a gaban alfarwa ta sujada daga gabas, su ne Musa, da Haruna da 'ya'yansa maza, waɗanda aka danƙa musu tafiyar da aikin Wuri Mai Tsarki, da dukan aikin da za a yi wa Isra'ilawa. Banda su, duk wanda ya je kusa da wurin sai a kashe shi.