Numbers 32:33 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Musa ya ba wa mutanen Gad, mutanen Ruben, da rabin mutanen Manasse ɗan Yusuf, masarautar Sihon, sarkin Amoriyawa, da masarautar Og na Bashan, dukan ƙasar, tare da biranenta da kuma yankunan da suke kewaye.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً مُوسَٰى يَبَامُتَنٜىٰنْ غَدْ دَ مُتَنٜىٰنْ رَعُبَيْنُ دَ رَبِنْ مُتَنٜىٰنْ مَنَسّٜىٰ طَنْ يُوسُڢَ يَنْكِنْ مُلْكٍ سَرْكِے سِهُوانْ نَ أَمُواْرِيَاوَا دَ يَنْكِنْ مُلْكٍ سَرْكِے عُواغْ نَ بَشَنْ، تَرٜىٰدَ غَرُرُوَنْسُ دَ يَنْكُنَنْ دَ دَا سُكٜىٰ ڧَرْڧَشِنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan Musa ya ba Gadawa, da Ra'ubainawa, da rabin mutanen Manassa, ɗan Yusufu, mulkin Sihon, Sarkin Amoriyawa, da mulkin Og, Sarkin Bashan, wato ƙasar da biranenta da karkaransu.