Numbers 35:25 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dole taro su kāre wanda ake zargi da kisa, daga mai bin hakkin jini. Su mai da shi birnin mafaka inda ya gudu ya tafi. Dole yă kasance a can sai mutuwar babban firist, wanda aka shafe da mai mai tsarki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تَرُوانْ جَمَعَ ذَاسُ كُٻُتَرْدَ مَيْ كِسَنْ كَيْ دَغَ حَنُّنْ مَيْبِنْ حَكِّنْ جِنِنْ طَنْعُوَنْسَ؞ سَعَنً سُمَيْدَ مَيْ كِسَنْ كَيْ ذُوَا غَرِنْ دَ دَا يَغُدُ نٜىٰمَنْ مَڢَكَا؞ ذَيْ ذَوْنَ أَوُرِنْ سَيْ لُواْكَثِنْ دَ بَبَّنْ ڢِرِسْتِ وَنْدَ عَكَ كٜىٰٻٜىٰ دَ مَنْ ڟَرْكِے يَمُتُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Taron jama'a za su ceci mai kisankan daga hannun mai bin hakkin jinin. Su komar da shi a birnin mafaka inda ya je neman mafaka. Zai zauna can sai lokacin da babban firist da aka keɓe da tsattsarkan mai ya rasu.