Numbers 36:3 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
To, a ce sun auri mutane daga waɗansu kabilan Isra’ilawa fa; ka ga, za a ɗebe gādonsu daga gādon kakanninmu a ƙara wa gādon kabilan mutanen da suka aura ke nan. Ta haka za a ɗebe sashe daga gādon da aka ba mu ke nan.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا عِدَنْ سُكَ عَوْرِ مُتَنٜىٰ دَغَ وَطَنْسُ ذُرِيَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ، تُواْ، ذَاعَ طَوْكِ غَادُوانْسُ دَغَ غَادُوانْ كَاكَنِّنْمُ عَبَا ذُرِيَرْ دَسُكَيِ عَوْرٜىٰ عَثِكِ؞ إِنْ حَكَ يَڢَرُ، كَغَنِ، أَنْ طَوْكِ غَادُوانْ دَغَ رَبُوانْ غَادُواْ نَكَاكَنِّنْمُ كٜىٰنَنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma idan suka auri waɗansu daga waɗansu kabilan jama'ar Isra'ila, wato za a ɗebe gādonsu daga gādon kakanninmu a ƙara wa gādon kabilan mutanen da suka aura, wato ka ga an ɗebe daga cikin namu gādo ke nan.