Numbers 4:12 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Za su ɗauki dukan kayayyakin da ake amfani da su a wuri mai tsarki, su nannaɗe su da zane mai ruwan shuɗi, su rufe shi da fatar shanun teku, sa’an nan a sa su a kan sandan ɗaukarsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَاسُ طَوْكِ دُكَنْ كَايَنْ عَيْكِنْ دَ عَكٜىٰيِنْ أَمْڢَانِ دَسُو أَ وُرِے مَيْ ڟَرْكِے، سُنَطٜىٰسُ دَ ذَانِ مَيْ كَلَرْ ضُوً بُلَ، سُرُڢٜىٰسُ دَ ڢَتُ مَاسُ ݣَوْ، سُكُمَ سَاسُ عَكَنْ ڢِرَمْ نَطَوْكَرْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Su ɗauki dukan kwanonin da ake amfani da su a Wuri Mai Tsarki, su sa su cikin shuɗin zane, sa'an nan su rufe su da fatun awaki, a sarƙafa su a sanda don a ɗauka.