Numbers 4:14 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan su sa a kansa dukan kayayyakin da aka yi amfani da su a bagaden, haɗe da farantai don wuta, cokula masu yatsu don nama, manyan cokula, da darunan yayyafawa. A kansa za su shimfiɗa murfi na fatun shanun teku, su zura sandunan ɗaukarsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَكَنْسَ ذَاسُسَا دُكَنْ كَايَنْ عَيْكِنْ دَ عَكٜىٰيِنْ أَمْڢَانِ دَسُو عَبَغَدٜىٰنْ، وَتُواْ ݣُونُواْنِ نَݣُوشِ غَرْوَشِنْ وُتَادَ ثُواْكُلَ مَاسُ يَڟُ دَ شٜىٰبُرْ دَ مَنْيَنْ ݣُونُواْنِ، وَتُواْ دُكَنْ كَايَنْ عَيْكِنْ بَغَدٜىٰنْ، سُكُمَ رُڢٜىٰشِ دَ ڢَتُ مَاسُ ݣَوْ؞ ذَاسُسَا وَبَغَدٜىٰنْ سَنْدُنَنْ طَوْكَرْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan su sa dukan kayayyakin bagaden a kansa waɗanda ake aiki da su a wurin, wato su farantai don wuta, da cokula masu yatsotsi, da manyan cokula, da daruna da dai dukan kayayyakin bagaden. Su kuma rufe bagaden da fatun awaki, sa'an nan su zura sandunan ɗaukarsa.