Numbers 5:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma in mutumin da aka yi wa laifin ba shi da ɗan’uwa na kusa da za a biya diyya saboda laifin, sai diyyar tă zama ta Ubangiji, dole kuma a ba wa firist, haɗe da ragon da za a yi kafara da shi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا عِدَنْ مُتُمِنْ دَ عَكَيِ مَسَ لَيْڢِے يَمُتُ، كُمَ بَاشِ دَ دَنْ‌غِ نَكُسَ وَنْدَ ذَاعَ مَيَرْ مَسَ أَبِنْدَ عَكَيِ ٻَرْنَ، تُواْ أَبِنْ يَذَمَ نَ يَهْوٜىٰهْ ؞ ذَاعَبَا ڢِرِسْتِ، حَطٜىٰ دَ ضَغُوانْ ڢَنْسَ وَنْدَ ذَاعَيِ ڧَٰعِدَرْ طَوْكَرْ أَلْحَكِنْ ذُنُوبِ دَشِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Idan wanda ya yi wa laifin ya rasu, ba shi kuma da wani dangi na kusa wanda za a ba diyyar, sai a kai diyyar gaban Ubangiji domin firist, tare da ragon hadaya, don yin kafarar da za a yi masa.